Monday, September 28, 2009

ABIN KAUNATA RASULULLAHI

ABIN KAUNATA RASULULLAHI(S.W.A)
-Muhammad Mahmud Yarima

1. Da sunan Jalla mai baiwa
Gwanin nan wanda yai kowa

2. Na ke son fara wakena
Da zan ma Mustafa nawa

3. Muhammadu dan Amina na
Imamul muttakiinawa

4. Salati hadda taslimi
Ga jinkan addananawa

5.Da alaye, sahabbai har
Da az’wajinsa kyawawa

6. Ina rokon Ka Ya ALLAH
Ka min Kyauta da ‘yar baiwa

7. Ta in zan yin yabon manzo
Da yin raddi ga arnawa

8. Ka ban ikon ta kai baiti
Dari cif babu yankewa

9. Ka ban dama ta in tsara
Ta hau tsaf babu karyewa

10. Ma- faa-ii-lun, Ma-faa-ii-lun
Ma’aunina ga tsarawa

11. A Fadin duniyar nan kaf
Gabas, yamma, arewawa

12. Zuwa yau dagga can farko
Bakar fata da lar’bawa

13. Ba ai da mai kamar kai ba
Cikin turarai da aj’mawa

14. A kyan hali da fuska ma
kawai kai ne ka burgewa

15. Ado nai gaskiya kullum
Kazib, bai kirkirantowa

16. Irin halin Aminullah
Ina mai ma Kwatantawa

17. Bale ma har a ce ya kai
Ga cimma Dan kuraishawa

18. Muhammad Sayyidul âlam
Uba gun duk talakkawa

19. A kyauta ba shi yin kwauro
A don tsoron talaucewa

20. Khalilullahi Dan lele
Na Allah mai azurtawa

21. A harka ba shi yin kwange
A zance ba ya hargowa

22. Liwa’ul hamdi sai dai kai
Maceci gun mu ran tsaiwa

23. Abin kauna Rasulullah
Abin bi babu tabewa

24. Kira na gunku al’umma
Ku tsinewa yahudawa

25. Da Ke zagin habibullah
Masoyin mai halittawa

26.Wabillah ! Kun kade arna
Mutan banza Amurkawa.

27. Mutan Den mark na fir’auna
Irin aikinku sai wawa

28. Da sauraran masu kin manzo
Diyan wofi faransawa

29. Masifu har bala’o’a
Ka jibga kan su daddaiwa

30. Ka dora kansu kaskancin
Da ba rana ta daukewa

31. Ku ce amin masallata
Ku amsa min da gaggawa

32.Ina arna la’an tattu
Da mushrikai, majusawa

33. Munafukkai da ‘yan tsafin
Bakar fata da turawa

34. Ku binne kanku don haushi
Muhammad ya wuce kowa

35. Mukami gun sa har ga kai
Munâjâti na ganawa

36. Da Jallallahu; can sammai
Ya keta babu kangewa

37. A arnan duniya kwata
Gaba dai ban cire daiwa

38. Mutane har da aljannu
Da mai ‘yanci da ma bawa

39. Arab ne ko bakar fata
Bamanagole da turkawa

40. Na farko har zuwa karshe
Suna tsoro Rasul nawa

41. Da zarar sun ji sunansa
Gaba dai dimaucewa

42. Bale ma har a ce yaki
Matsafa sai fa watsewa

43. Su ruga can cikin daji
Ya karnai basu waigowa

44. Muhammad jarumi gwarzo
A fama baya juyawa

45. Kwamanda ne a gun yaki
Tsayayye babu rugawa

46.A komai kai na ke son bi
Ina zan so musanyawa

47. Na’am, sunnarka dadin bi
Da sauki ba tsanantawa

48. Ina ma da ace na zo
A loton Dan Hishamawa

49. Makaucewar idanuna
Ya zan ya sami warkewa

50. Dalilin ban ga Manzo ba
Makaho ne ni, baubawa

51. Rashin in gan ka Ya Manzo
Ya kan sa in ta kokawa

52. Uhm! Ni dai takaicina
Rashin yakar badardawa

53. Da ban sa’ar zuwa nai ba
A ban lambar shahidawa

54. Mahaifina a gaisheka
Ina kauna da godewa

55. Da sunan nan da kas sa min
Irin sunansa kyakkyawa

56. Ina kaunar Ka Ya Manzo
Da fatan in zamantowa

57. Cikin gaiyar masoyanka
A can ranar lisaftawa

58. Ina shauki da begenka
Khalilin mai hukuntawa

59. Dado yardarKa Ya Allah
A kan az’waj da ah'lawa

60. Su Hafsat, A’isha, Saudat
Da Ramlat ba ni mantawa
61. Da Zainab Bintu Jah’shin har
Da Zainab ‘yar Khuzaimawa

62. Juwairiyya, Safiyya har
Khadijat, Ummu Salmawa

63. Da Maimunat diyar Haris
Cikon sha dai a kirgawa

64. Uwaye ne a gun kowa
Da kowa banda gaulawa

65. Bakin arne da mai zagin
Su; zindiki, kare gawa

66. Ga ‘ya’ya nai na kirkin nan
A yanzun zan lisaftowa

67. Batula: Fâtima Zahra
Da ‘ya’yan gunta Husnawa

68. Su Kasim, Ummul Khulsumin,
Mu’azzam dan kusaiyawa

69. Rukaiya har da Abdullah
Da Zainab ‘ya ta nunawa

70. Iyalai ne gidan Manzo
Na Allah ba musantawa

71. Ina kaunarku ba shakka
Gaba dai babu warewa

72. Zunubbaina na ke hange
Da wautata da sabawa

73. Tunanin kar su kakkange
Ni; kaiwa gun ka dan baiwa

74. A ranar nan da bayi duk
Kiyaman ba tsugunnawa

75. Ina rokon Ka Ya Allah
Ka ban dama ta ganawa

76. Da manzo mai ruwan tafki
Na kausar ba musantawa

77. Ina biro da harshena
Ku zo nan mui ta tsinewa

78. Yahudawa da ‘yan iska
Mutan turai, nasarawa

79. Haba! Sun zagi Manzona
Ta ya ya za ni kyalewa

80. Ina barranta da nisanta
Da dukkannin kiristawa

81. Da arnan nan na can Den mak
Miyagun har faransawa

82. A tsammaninsu taronsu
Na dangi babu rushewa

83. A duk taron da za kui kaf
ku san karshenku watsewa

84. A harka baya gaggawa
A zance baya hargowa

85. Irin Manzonmu mata duk
Na yau sun kasa haihowa

86. Ina! Wane mutum?, ai har
Kiyama ba a samowa

87. Ba ai tamkarsa can da ba
Iri nai ba a karawa

88. Uwata har da babana
Su zan fansa ga Kyakkyawa

89. Muhammad mai dubun kyauta
Na Hafsat Dan Kilabawa

90. Hakika ni ba zan kai ba
Irin Hassaan a wakewa

91. Da yin raddi ga arna duk
Ina fatan misaltawa

92. Ina gaida ka ya Hassaan
Mawakin mai madinâwa

93. A gun Allah Ta’ala dai
Nake kakkara godewa

94. Da ikon nan da yab ba ni
Na yin raddi ga arnawa

95. Ta’ala Kai dadin tsira
Ga Mâhï Wanda bai rowa

96. Muhammad mai cikar kira
Na Ramlat Dan kinanawa

97. A nan ne zan tsaya; ta kai
Dari cif babu yankewa

98. Nakumbon Malama Asï
Abokin dan rikadawa

99. Akan ce mai Yarimah Dan:
Gidan Maude na Madâwâ

100. Ya tsaro wanga baitoci
A reras babu tsinkewa

Thursday, September 24, 2009

MY WIFE should be

MY WIFE
Should be

Friendly and calm not termagant
Benign and patient not lousy
Kind and humble not arrogant
Slender and pretty not clumsy

Mild and wise not illiterate
Esteem and cheerful not worthless
Good and content not always in debt
Healthy and caring not careless

Just and honest not eloper
Talking and whispering not in jargon
Chatting and teasing not in anger
Peaceful and happy not forlorn

Native lady not immigrant
Skilful and tidy not Slovene
Fine and graceful not recalcitrant
Dressy and demure not vixen

FURFURA

FURFURA

1.
Ya makagin duk halittu
Wanda ke baiwar sarautu
Yai musulmi har batattu
Yay yi mata masu shantu
Kai na fara anbatowa

2.
Kara tsira mai yawaita
Gun Rasul mai kyau da tsafta
Har da alayensa kwata
Sa sahabbai masu bauta
Masu kaunar kyautatawa

3.
Duk da cewa shekaruna
‘Yan kadan ne kankanana
Furfura ta sauka kaina
Gargadi in gyara kaina
Yanzu kar in zan sakewa

4.
Zamani na wuwwucewa
Mautu ma na zagayawa
Ga ni na dau furfurewa
Al’bishir ke nan ga cewa
Mautu ce ke mammatsowa

5.
Dan jikina ya yi laushi
Shekaru sun tankwara shi
Furfura ta canza gashi
Yai fari tamkar na leshi
Yanzu sai dai rirrinawa


6.
Dole in bar shantakewa
Babu zancen shakatawa
Jin kida har rausayawa
Balbu sauran gulmatawa
Sai ibada ba tsayawa

7.
Sai su azkar, nafiloli
Yin tahajjud, aiki jamili
Bin tafarki sak a fili
Banda aiki ba dalili
Kar na zan dan kirkirawa

8.
Sai lizimtar yin salati
Kauracewa shirya “Party”
Banda bin mata a titi
Kar na koma jin su sauti
Furfura na tsawatarwa

9.
Da tunanina da homa
Bai wuce mata da gulma
Na haye doki na zulma
Na ki hankalta na koma
Sai kwatsam ga furfurewa

10.
Malaman kirki na sunna
Sun fada kar mui ta barna
Kar mu koma mui ta sauna
Kar mu shashance mu zauna
Lokaci na kukkurewa


11.
Nai biris na kama Danni
Kurciya na zizziga ni
Babu aune sai fa ga ni
Yanzu don Allah ku ji ni
Furfura ta mamayewa

12.
Na nutse neman bareyi
Na yi sabo masu nauyi
Ga shi gabbai sun yi sanyi
Taimakan Allah ga sauyi
In bi hanyar kyautatawa

13.
Jallah Kai ne Al’gafuru
Kar ka sa in zan mariru
Masu yin tubar muzuru
Ko ko tsufan “John”a zuru
Ma su sabo ba kulawa

14.
Rabbi kai n eke da jannah
Taimakan aiki na jannah
‘Yar wazifa kar na daina
Hadda wurdin nan na sunnah
Har zuwa na can kushewa

15.
Rabbi bawan nan Nakumba
Dan gidan Zainab da Abba
Ke bidar af’warKa babba
Babu shakka ya fa duba
Nesa ce ke kukkusowa

16.
Zan tsaya nan don na huta
Wag ga waka wadda nai ta
Baituka sha shidda kwata;
Gargadi don zuciyata
Kar ta ja min babbakewa