Monday, August 5, 2013

ABIN KAUNATA LITTAFIN ALLAH: ALKUR'ANI

ABIN KAUNATA LITTAFIN ALLAH
A duk lokacin da tarihi ya maimaita kansa, ana son mutane su koma su dubi tarihin don su samo hanyar gyara, in abin ya shafi gyara ne. idan kuwa ya shafi karfafawa ne, sai a yi hakan.
A shekara ta goma sha biyu bayan hijira aka samu afkuwar yakin yamama, wanda a cikinsa ne aka kashe mahaddatan Alkur’ani daga cikin sahabbai masu dimbin yawa. A yau duk mai hankali ya shaida irin kisar mahaddata Alkur’ani da aka yi a Maiduguri. Babu shakka Allah kadai Ya san adadin mahaddata da makarantan Alkur’ani da aka kashe. Ba su ji ba, ba su gani ba, ba ci ba, ba su sha ba.
Bayan yakin yamama, sahabbai sun yi kokari wajen ganin cewa Alkur’ani bai salwanta bat a hanyar kasha mahaddatansa, suka yi aiki tukuru wajen tattarawa da rubuta alkur’ani a waje daya, wanda gajiyarsa ne muke ci a yau.
To mu kuma me za mu yi wa Alkur’ani ganin yadda aka rasa dimbin mahaddatansa a waki’ar da ta faru?
KOKARIN DA ZA MU YI SHINE, DON ALLAH, KOWANE GIDA NA MUSULMI DA KE WANNAN KASAR A TABBATAR DA CEWA AN SAMAR DA MAHADDATAN KUR’ANI A KALLA GUDA UKU. SANNAN YA ZAMA DUK MUTANEN GIDAN MAKARANTAN KUR’ANI NE.
Wannan shi ne kadai abinda za mu yi don ganin wanzuwar Kur’ani, kuma shi ne diyyar ko tukuicin da za mu biya wadanda aka kasha da shi.

HANYAR KYAUTATA DANGANTAKAR MU DA ALKUR’ANI
Shin ko muna cikin irin mutanen nan da ke karanta Kur’ani jefi-jefi, ko kuma ma ba ma karanta shi? Idan haka ne, ba ma tsoron ranar da Manzon Allah (saw) zai kai karar mu a gaban Allah (swa), ya nuna ma Allah mu, yana mai cewa Ya Ubangiji, wadannan sune suka kaurace ma Alkur’ani (a duniya).
Wadannan wasu hanyoyi ne da za mu bi wajen ganin mun gyara dangantakar mu da Alkur’ani.
1.     Mu tabbatar da mun je mun koyi karatunsa a gaban malamai kwararru masana karatunsa da fassararsa.

2.     Niyyar mu ta karatun Alku’ani ta zama don Allah ne kawai, ba don neman shahara ba. Sannnan mu tabbatar da cewa duk abinda muka karanta  mun yi aiki da shi gwargwadon iyawarmu.

3.     Idan ba ma iya daukar lokaci mai tsawo muna karanta shi, to mu fara da karanta shi na minti biyar a kowace rana. Da yardar Allah wannan minti biyar din zai koma minti talatin, har ya kai lokcin da za mu iya kwashe awoyi muna karanta shi.

4.      Mu tabbatar da muna sanin abinda muke karantawa. Ya kamata ace kowane gidan musulmi akwai Alkur’ani mai fassara da yaren da mutum ya ke ji.

5.     Kada mu takaitu ga karatunsa kawai, mu yi kokari mu dinga sauraren karatunsa a bakin wasunmu ko a kaset ko kuma a CD  

6.     Babban abu mafi muhimmanci shine addu’a. Mu yawaita rokon Allah Ya sa mu zama daga cikin masu karatun littafinSa dare da rana, Ya bamu ikon sanin ma’anarsa, Ya kuma azurata mu da yin aiki da abinda muke karantawa.

HANYAR GYARA KARATUN ALKUR’ANI
Babu wata hanyar da za mu gyara karatun Alku’ani in ba ta hanyar sanin tajwidi ba. Babban abu kuwa shine sanin mafitar haruffan larabci. Don in har za mu karanta kur’ani da lahajar mu ta Hausa to, babu shakka za mu dinga caccanza ma’anonin Kur’ani.
Misali, inda Allah Madaukakin Sarki ke cewa
1.     إنه عليم بذات الصدور
idan mutum ya karanta da hamza,  أليم  ya canza ma’anar daga Allah masani ne  ya koma Allah mai radadi ne. Subhanallah

  2. Haka nan inda Allah (swa) yake cewa مخلصين له الدين  idan mutum ya karanta da sinun  مخلسين ya canza ma’anar daga masu yi tsantsa saboda Allah zuwa masu yankan Aljihu. Subhanallah

3.     Haka nan inda Allah ke cewa وضل عنهم ما كانو يفترون   
Da mutum zai karanta da dalun      ودل shi ke nan mutum ya canza ma’anar daga  ya bace musu….  zuwa ya yi musu nuni ……

4.       Har ila yau da mutum zai karanta fadin Allah (swa)
 لا تخونوالله والرسول da kafun madadin kha’un ,   تكونو  لا ma’anar ta canza daga: kada ku ha’inci Allah da Manzon Allah zuwa kada ku zama Allah da Manzon Allah.
Da sauran irinsu.
Ashe ke nan dole ne mu koyi yadda ake furta kowane harafi na larabci don mu tsira daga irin wadannan kura-kuran

Aljazari na cewa:
“Dolen dole ne akan (makarantan Alkur’ani )
Ya zama abu na farko tun kafin su fara (karatun alkur’ani) su san
Mafitar haruffofa da siffofinsu ………
Wanda duk baya karanta kur’ani da tajawidi (ya zama) mai laifi
Domin da tajwidinsa aka saukar da shi, kuma a hakan ya kawo zuwa gare mu.”

بســـــــــــــم اللــــــــه الرحمــــــــان الرحيـــــــــــــم
اللهم رب السماوات السبع و رب العرش العظيم، ربنا ورب كل شىء فالق الحب والنوى منزل التـــــــــــــوراة والإنجيل و القرآن, أنت الأول فليس فبلك شـــــــــيء و أنت الآخر فليس بعدك شيء، و أنت الظاهر فليس فوقك شيء و أنت الباطن فليس دونك شيء
اللهم صل على محمد و على أهل بيته، وعلى أزواجه وذرياته، كما صليت على آل إبراهيم، إنك حميد مجيد، و بارك على محمد وعلى آل بيته، وعلى أزواجـــــــه و ذرياته، كماباركت على آل إبراهيم، إنك حميد مجيد
اللهم ربنا تقبل منا ختم القرآن و تجاوز عنا ما كـــان فى تلاوته من السهو والنسيان واكتبه منا على التمـام والكمال المهذب من كل الألحان. اللهم اجعل القــرآن لنا فى الدنيا قرينا، وفى القبر مؤنسا، وفى القيامـــــة شفيعا، وعلى الصراط نورا، و إلى الجنة رفيقا، ومن النار سترا و حجابا و الى الخيرات دليلا و إماما يـــا أكرم اللأكرمين. اللهم علمنا منه ما جهلنا وذكرنا منه ما نسينا واروقنا تلاوته وحفظه تأويله آناء الليــــــــل وأطراف النهار على الوجه الذى يرضيك عنا يا رب العالمين. اللهم اجعلنا من الذين إذا تليت عليهم ءاياتك زادتهم إيمانا. اللهم اغفر لإخوانن الذين سبقونا بالإيمان, وخصوصاإخواننا حفظ القرآن الذين قتلوا فى ميدغرى ظلما
اللهم يا خير الراحمين ارحمنا، ويا خير الغافريـــــــن اغفر لنا، ويا خير الرازقين ارزقنا و يا خير الفاتحين افتح لنا أبواب رحمتك كلها و خير الناصريـــــــــــن انصرنا، ويا خير حافظ احفظنا بما تحفظ به عبــادك الصالحين
اللهم بدل عسرنا يسرا، وضيقناسعة, وفقرنا عنـــى, وضعفنا قوة, وخوفنا أمنا وسلاما واستقرارا لنـــــــا ولسائر المسلمين يا رب العالمين
اللهم إنا نسألك خشيتك فى الغيب و الشهادة و نسألك كلمة الحق فى الغضب والرضى،ونسألك القصد فى الفقر و الغنى، ونسألك نعيما لا ينفد و قرة عيـــن لا تنقطع, ونسألك الرضا بعد القضاء وبرد العيش بعد الموت ومرافقة نبيك محمد صلى الله عليه وآله وسلم
ولذة النظر إلى وجهك والشوق إلى لقائك فى غيــــر ضراء مضر ولا فتنة مضلة
اللهم إنا نسألك بأنا نشهد أن لا إله إلا أنت الأحــــــد الصمد الذى لم يلد و لم يولد ولم يكن له كفوا أحـــد, يــــا ذالجلال والإكرام يا حي يا قيوم أن تفتح لأدعيتنا أبواب الإجابة يا من إذا سأله المضطر أجابه يامــــــن فلق البحر لموسى يا فالق الحب والنوى يا حي يا قيوم يــــا ذالجلال والإكرام. ربنا آتنا فى الدنيا حسنة و فى الآخرة حسنة و قنا عذاب النار
اللهم صل على محمد و على أهل بيته، وعلى أزواجه وذرياته، كما صليت على آل إبراهيم، إنك حميد مجيد، و بارك على محمد وعلى آل بيته، وعلى أزواجـــــــه وذرياته، كماباركت على آل إبراهيم، إنك حميد مجيــد

MUSULUNCI KAWAI


Bismillahi r rahmani r rahiim
Al’ummar musulmi sun kasance al’umma daya a zamanin Manzon Allah (saw) kamar yadda Allah (swa) Ya fada a cikin Suratul Anbiya’I aya ta 92:
“LALLAI WANNA AL’UMMAR TAKU AL’UMMA CE GUDA DAYA, KUMA NINE UBANGIJINKU, DON HAKA KU BAUTA MINI.”
Tun a zamanin Annabin rahama (saw) Yahudawa da munafukai suke ta kokarin raba kan musulmi da kawo musu rudani da sabani a cikin addininsu, har akwai lokcin da munafukai suka tunzura mutanen Madina musulmai ta hanyar tuna musu abinda ya gudana a tsakaninsu  lokacin jahiliyya na kiyayya da kasha-kashen rayuka. Nan fa hankali ya tashi, aka tashi za’a buga, amma Annabi (saw) ya tsawartar, ya tunasar da su ni’imar Allah da Ya yi  musu na hada su a waje guda a karkashin Kalmar musulunci. Da haka ne Allah Ya kawar da wannan mugun kullin na munafukai.
Haka al’ummar musulmi suka zauna a al’umma daya har karnonin nan masu albarka da falala suka wuce. Karnonin da Annabi (saw) ya ce sune mafi alkhairin zamunna. [ Bukhari 3/3650,3651]  A wadannan zamunnan, ba wata barna da zata shigo cikin musulunci sai an kawar da ita da karfin hujjojin ilimi na Alkur’ani da sunnonin Manzon Allah (saw) da kuma karfin mulkin musulunci.
Bayan wadannan karnona masu albarka, sai mulkin sarakunan musulunci ya biyo baya. Lokacin da musulmai suka cudanya da wasu mabiya addinai daban, wadanda ba musulmai ba. A haka ne har aka kai lokacin da aka fara fassara wasu littattafan wadannan arnan zuwa harshen larabci. Daga nan ne aka samu barakar da aka shigo da wasu abubuwa cikin musulunci har aka samu rabe-rabe da kungiyoyin musulmai. Abin mamaki kuma shine kowane bangare yana alfahari da kungiyarsa, yana ganin cewa duk wanda ba su ba to, batacce ne. Haka kuma za mu ci gaba da tafiya har illa ma sha Allahu. Domin Allah madaukakin sarki cewa ya yi:
“…SAI DAI BA ZA SU GUSHE BA SUNA SASSABAWA, SAI DAI WANDA UBANGIJINKA YA JIKANSA, DON HAKA NE MA AKA HALICCE SU…”[Suratu  HUD: 188-118]
Sannan Annabi (saw) ya ce, ….wannan al’ummar sai ta kasu zuwa kasha saba’in da uku ….. [Tirmizi 5/2641 ]
Annabi (saw) ya ce, “duk wanda ya rayu a cikinku, sai ya ga sabani mai yawa.” Allahu Akbar! Annabi ya yi gaskiya, dama mai gaskiya ne abin gaskatawa. A yau sabani ya kai har wani bangare na ba shugabansu matsayin Allah na cewa bai Haifa ba ba’a haife shi ba.  A hakan suke alfahari su ganin sune masu gaskiya. Allah Ya shiryar da mu. Amin

INA MAFITA?
A lokacin da Annabi (saw) ya ce wannan al’ummar zata karkasu kasha saba’in da uku kuma  dukkansu ‘yan wuta ne sai daya kawai, sahabbai sun tambaye shi “wacce ce wannan?” sai Annabi (saw) ya ce, “Wadanda suka tsaya akan abinda ni da sahabbaina muka tsaya akai.” Wannan it ace mafita.
Annabi da sahabbansa dai sun rayu ne a kan musulunci kuma akansa suka bar duniya. Suna masu bin Alkur’ani da sunnar Manzon Allah (saw). Wannan shine musuluncin da Allah Ya yardar mana da mu bi shi. Shine kuma addinin da Annabi Ibrahim ya yi ma diyansa wasiya da shi, inda ya ke cewa: “ALLAH YA ZABAR MUKU ADDINI, DON HAKA KADA KU YARDA KU MUTU SAI KUNA MUSULMI” [suratul Baqara:132] ba ‘yan kungiya ba. Babu wani suna da ya kamata musulmi ya yi alfahari da shi fiye da musulunci. Don haka ne ma Annabin Allah Yusuf ya yi addu’ar cewa “….. ( Ya Allah) Ka karbi raina ina musulmi ka kuma hada ni da salihai.” [Suratu Yusuf]
Allah Ka ba mu ikon bin addininKa kamar yadda Annabi ya bar sahabbansa akai Amin.
M.M. Yarima
Ramadan 11,  1434