Sunday, November 29, 2009

MY BELOVED: PROPHET MUHAMMAD (SAW)

I love you more than my father
I love you more than my mother
Ilove you more than my wife
I love you more than my children
In fact, I love you more than anybody living on earth
Or dead and buried beneath the earth







Friday, November 27, 2009

GODIYA GA MASOYANA

GODIYA GA MASOYANA
-muhammad Mahmud Yarima


Masoyana mutan kirki
Ina kaunar ku ba wai ba

Iyayena ba zan manta
Da tarbiyyarku mai haiba

Da kun kai min a
don kar in
Zamo wawa kamar dabba

Cikin kauna ku kai reno
Gurina ba da wasa ba

Iyayena fa na gode
Musamman gun ka ya baba

A gun Dan Shehu ban yunwa
Mijin Gajeje ‘yar baba

Da sallah ban kishin nama
Tuwona ba kire ne ba

Atikun Gaje na gode
Ba zan manta da kauna ba

Ina zan mance malamman
Da sun kai kokari babba

Wajen koyar da ni ilmin
Da yassa nazzamo babba


Kamar Nuran Yahayyan nan
Na kuramii ba dolo ba


Su Malam Murtala Giwa,
Hisabi sai fa gun Garba;

Su Albani da Dan Mora
Ina, ba za ni mance ba

Umar Fallati na gode
Kwarai ba dan kadan nan ba

Alarrammah Sulaiman ma
Da Idi ba gajere ba

Wadannan malaman nawa
Da ma duk wanda ban sa ba

Mutane ne da shaihunnai
Na Allah ba na shaidan ba

Uwar Zainab uwar kirki
Rukaiyah ‘yar Nuhun Abba

Halin girma da dattakon
Rukaiya ba kadan ne ba

Uwa gun Abdu: Ya Hauwa
Kululun A’i ‘yar baba

Alasan kai da matar nan
Jamila taka mai haiba

Muhammad Zoogitex dan nan
Da bai wasa da yin zamba


Su kanwata uwar Ummah
Da yayana Habu Garba

Ku sa min Rabi yayata
Sahun farko a mahbuba

Shi Ibrahima yaya ne
Na madallah fa ba tir ba

Su Abdullahi, Sai Dijen
Gidan Bagen mu ba wai ba

Diya ke nan na babana
Sadauki ba baliidii ba

Amina ‘yar gidan Malam
Lawal ba jahila ce ba

Ina godewa dukkannin
Ku; sosai ba da wargi ba

Ina Shukran kwarai; tabbas
Ina begenku ba zur ba

A Ya Allah Ka sakanka-
Wa; dukkanninsu ba dai ba.

Bakar karya kazama tir!
Da halayenki ke dabba

Kucaka mai kamar jaba
Mijin sam bai yi dace ba

A nan zan tsaida wakar nan
Gajera ba dawiilaa ba

Masoyana da ban sa ba
Cikin waken ga na tuba

Ku yafan kar ku zarge ni
Lalurar kafiya; Garba