ME YA KAWO HAKA??!!
Na dade ina ta tambayar kaina wasu
tambayoyi a zuci, har sai da ya kai ga cewa zancen zucina ya fito fili. Amma
har yanzu da alkalamina ke rubuta wannan zancen zucin nawa, ban gano amsar da
zan ba kaina ba.
Ku taimake ni don mu gano amsar
tare.
Tambayar farko:
A zamanin da, malaman addini kan yi
amfani da minti biyar kacal, wajen yin wa’azi ga mutane, wa’azin ya ratsa
jikinsu, ka ga mutane na kuka suna qauracewa savon Allah ta sanadiyyar wannan
wa’azin. Amma me ya sa a yau nake kwashe awa biyar ina wa’azi mai cike da
balaga da hikima da qwarewa ta ilimi, amma wa’azin bai ratsa zuciyar mutane
balle su bar abinda suke yi na savon Allah???!!! Ka ga idanuwanmu
qarmadagau???!!!
Tambaya ta biyu:
A da, kakata ta haqura ta zauna a
gidan mijinta cikin wadatar zuci, ta gamsu da duk abinda kakana zai kawo mata.
Amma me ya sa matata a yau ta lashi takobin sai ta fita ta yi aiki, da sunan
wai ba komi zan iya yi mata ba, alhali ba na gaza ba ne???!!!
Tambaya ta uku:
Magabatanmu mutane ne masu
mutunci da izza. Su ke faxa aji, su ke gitta kara ba’a tsallaka musu, sune
iyayen gidan wasu, ba’a yi musu kallon raini. To me ya sa a yau raini da
wulakanci ya baibaye mu, ya lulluve mu???!!! A cikin masu raina mun ma har da
bayin kakanninmu!!!
Tambaya ta huxu:
A da za ka ga duk inda musulmi ya
gamu da xanuwansa musulmi yana xaukarsa tamkar xan gidansu ne uwa xaya uba
xaya. Ina irin wannan ‘yanuwantakar ina take a yau???!!!
Tambaya ta biyar:
A da Malamai da almajirai kowa na
fafutukar neman lahira ne kawai, ba su siyar da addininsu don samun abin duniya
qasqantacce, amma me ya sa a yau ni da malamaina ba mu da aikin yi sai ci da
addini???!!!
Tambaya ta shida:
A da idan Musulmi xaya ya shiga
wata damuwa gaba xaya za ka ga ‘yanuwansa musulmai sun shiga wannan damuwar;
idan kuwa ya faxa hannun arna ne to ko za su qare sai sun je sun ceto wannan
xanuwa musulmin. Amma me ya sa a yau mu ke komawa gefe idan wani ko wasu
‘yanuwa suka faxa cikin musiba???!!! Sai abin ya wuce mu kai mu su tsummokara
da garin rogo!!!
Wallahi ba wani abu da zai gyara
mu in ba abin da ya gyara mutanen farko ba.
Ba wata hanya da za mu bi
martabarmu ta dawo in ba mun koma mun kama koyarwar addininmu ba sau da qafa.
No comments:
Post a Comment