Friday, January 2, 2015

ZANCEN GASKIYA



Zancen Gaskiya
﴿ظهرالسد فى البر والبحر بما كسبت أيدى الناس ليذيقهم بعض الذى عملوا﴾
A lokacin da zan rubuta wannan takarda, babu shakka alqalamina da idanuwana na  kukan baqin cikin yadda a yau musulmai suka tsinci kansu musamman a Najeriya da kuma duniya baki xaya.
Na san cewa wannan takardar za ta sha tsokaci, gyara, qarin bayani, sharhi har ma da raddi. Ina roqon ‘yan uwana ma su yin raddi da su yi raddinsu a bisa adalci da tsoron Allah.
Mun ximauce muna neman mafita daga halin da muka tsinci kanmu a yau. Amma duk wanda ka zauna kana hira da shi sai ka ji yana cewa ai shekarar 2015 ba za mu yarda ba sai mun kayar da Mai-Nasara na yankin inyamirai. Tunaninmu gaba xaya ya taqaitu ga samun shugaban da za’a daina kashe mu, mu samu kudi da kwanciyar hankali. Ba ma tunanin ya ya zamu dawo da martabar addinin Musulunci a qasar; mu dai a daina kashe mu, mu ci gaba da kasuwancinmu da tara dukiya da mata.
Ina rantsuwa da sunan Allah, duk wani uzuri da za mu yi ta ba kanmu, da duk wata hila da kwana-kwana ba za su fitar da mu ba sai mun koma ga addinin Allah, ya zama Shari’ar Allah ita ke motsi a qasar. Allah Ya sa a fahimce ni a bayanai na da za su zo a gaba.
Bari mu kalli qasar gaba xaya ta fuskar:
 a) Shugabanci
Haqiqa duk mai hankali ya san cewa babu wani tsarin mulki babba da ake bi a duniya na dimokaraxiya ko mulkin soja wanda ba’a yi ba a wannan qasar tamu Najeriya, amma babu wani sakamako mai kyau da suka haifar in ba kashe shugabanin kirki ba, ruguza qasa da son maida ita kan wani tafarkin da bai dace da mu ba. Tsarin mulki xaya ya rage wanda ba’a yi ba a Najeriya, kuma ina rantsuwa da sunan Allah shine tsarin mulkin da zai kawo dukkan jin daxi da adalci da zaman lafiya mai xorewa a wannan qasar. Wannan tsarin shine Mulkin shari’ar musulunci. Sai dai abin tambaya a nan shine shin da irin wannan demokaraxiyar za’a samar da mulkin musulunci a Najeriya??!!
Wallahi a tarihin duniya ba’a tava yin haka ba. Ai ya ishe mu kyakkyawan misali abinda ya faru a qasar Misra (Egypt). Idan can Egypt ya yi mana nisa, to mu tambayi kanmu da kanmu: Ina makomar shari’ar Zamfara da sauran jihohin arewa?!
A kullum kira ake ta yi cewa a je ayi rajista, a jefa quri’a, mu zavi mutanen kirki masu kishin qasa, ba don komi ba sai don a samu zaman lafiya, walwala da qaruwar arziki. Wani lokaci har mu kan ce “Ai in ba zaman lafiya a qasa ko addinin ma ba za’a yi yadda ya dace ba.” A dai-dai lokacin mun manta da faxin Allah cewa:
﴿... وَالْفِتْنَةُ أَشَدُّمِنَ الْقَتْلِ
ma’ana: “Yin kafirci (a bayan qasa) shi ya fi yaqi tsanani”
Ai dai ga shi nan! Kullum siyasar muke yi, zaven mu ke yi, amma kullum cikin wahala mu ke qara shiga. Daga qarshe, kowa ya ga inda demokaraxiya ta kai mu a yau.  Abin mamaki, waxanda mu ka zava sune jagororin qasar, amma kuma ga musibu sun baibayemu. Anya! Ba wani abu kuwa??!! Anya! Ba’a kauce hanyar ba??!! Idan mun ce ma za mu yi demokaraxiyar a bisa lalura, to me ya sa ba za mu xauki shawarar da babban malami Muhammad Auwal Adam Albani ya ba musulmin Najeriya ba? [1]
A wajen duk wani musulmi mai kwana da tunanin addinin musulunci a ransa ya san cewa hanya xaya ce za ta kai mu ga tabbatar da addininmu a wannan qasar, sai dai a   kullum gudunta mu ke yi, muna cewa wai ba mu da qarfi, lokaci bai yi ba, sai dai kurin cewa ai muna da yawa a qasar. Hanyar kawai ita ce JIHADI. Wai! Tabxijan! a nan na san da yawan musulmai za su ce: kun ji wani mahaukaci, me muke da shi da za mu yi jihadi? Ina rantsuwa da sunan Allah, wannan xabi’ar ta sa muka manta da cewa jihadi wanzajje ne har zuwa tashin qiyama. Na cika da mamaki, ranar 17/8/2014 mu na karatu a makarantar islamiyya babin janaza. Da aka yi maganar yadda ake rufe shahidai, sai wata mata ta ce “wannan karatun mutanen da ne don yanzu ba jihadi.[2] Ka ga har an manta da cewa Annabi  (s) ya ce:
مَنْ مَاتَ وَلـَمْ يَغْزُ وَلـَمْ يـُحَدِّثْ نَفْسَهُ بِهِ مَاتَ عَلَى شُعْبَةٍ مِنْ نِفَاقٍ. رواه مسلم
Ma’ana:
Wanda duk ya mutu bai yi jihadi ba, kuma
bai  ma sa a ransa  cewa zai yi jihadi ba, to,
ya  mutu  a  wani  bangare  na   munafunci.
  
Jama’a da gaske na ke yi ina nufin jihadi na gaskiya, ba “jihad week” ba wanda ake barinsa a “campus” in an gama makarantar, ba jihadin baki ba. waxannan suna daga cikin abubuwan da suka jawo mana halin da muke ciki. Eh mana! Mun yi ta kurarin jihadi da baki kawai a qasar nan, wanda hakan ya tsorata wasu mutane a qasar, su ka shiga tara makamai, daga qarshe da suka gano abin duk bula ne, sai suka afka mana da kisa da walaqanci a wasu garuruwan arewacin Najeriya.
Allah Ka nuna mana ranar da za mu samu shugaba tsayayye wanda duk mutanen Najeirya za su yi masa mubaya’a ta yadda in ya yi umurni da mu fito, shi ke nan an gama. Allah Ka amsa mana. Amin!
A yau gaba xaya mutanen Najeriya sun makauce suna neman canjin gwamnati. Amma ba gwamnatin addini ba; su dai kawai a samu jin daxi da walwala. A maimakon musulmi su yi tunanin ya ya za’a ce musulunci ya mulki Najeriya, sai suma kawai suka koma suka kama tafarkin kafirar siyasar Najeriya, kai da qafa.
Mu tuna in mun manta cewa tunda Najeriya ta samu ‘yancin kai har zuwa yau, kafirci ke mulkin Najeriya kuma shi ke jan ragamarsa yadda ya so a qasar. Me yasa na ce haka? Ta yiwu wani ya ce ia musulmi sun sha yin shugabanci a Najeriya. Tabbas haka ne, amma ai ba da shari’ar Allah suka yi shugabancin ba. Kuma ba a lokacin mulkin xaya daga cikin musulman ba ne aka so a sa qasar cikin qungiyar qasashen musulmi na duniya ba? Amma da qungiyar arnan Najeriya ta ce ba ta yarda ba, haka nan aka kashe maganar har hazal yaum.  Dubi yadda arnan arewa suka afka ma musulmi a garuruwan Jos da Yalwan Shandam …. a nan arewacin Najeriya, suka kashe mutanenmu, suka qona dukiyoyinmu, suka kwashe matayenmu waxanda har yau suna can a hannunsu amma ba abinda aka yi. Gwamnati ba ta yi komai ba, mu kuma son duniya da tsoron mutuwa sun hana mu yin wani abu; kamar yadda Annabi (saw) ya faxa. Dubi irin kisar da suka yi ma musulmi a ranar sallah. Wai ina ‘yanuwantakar musulunci da ke tsakaninmu, wanda abin nan ya afku, ba xaya ba ba biyu ba, amma ba wani xauki da musulman qasar nan suka kai. Sai da aka gama abinda aka yi mu ka tara tsummokara da garin rogo mu kai musu. Abinda muka iya ke nan.  A yau kuwa Mai-Nasara na yankin inyamirai da qungiyar arnan Najeriya sun haxa kai sai sun ga bayanmu. Ba su son su ga muna addininmu. A nan na ke son ‘yan-uwa musulmi su san cewa samu daular duniya a qarqashin rashin bin dokar Allah, wahala ne kawai. Allah Ya kai haske qabarin Alfazazi da ya ce:
إِﺫَاالدِّينُ لَمْ يَكْمُلْ فَلاَ كَانَتِ الدُّنْيَا
Idan har ba za’a yi addinin (Allah) ba (a bayan qasa) to, babu amfanin wanzuwar duniya (gwamma duniyar ta tashi)    
Ya ku ‘yan uwana musulmin Najeriya, muna tunanin a yau idan aka buga kugen siyasa, muka zavi xan arewa musulmi, shi ke nan arnan nan za su bar mu a irin qarfi da xaurin gindin da suke da shi a qasar da sauran qasahen duniya masu goyon bayan ta’addanci?! Qarfinsu a yau ya kai ga su yi odar makamai jirgi guda wanda gwamnatin tarayya ce kawai zata iya sayen irinsu, kuma huxxar cinikinsu ma sai qasa da qasa.
Sai dai qungiyar CAN ba ta yi laifi ba. Eh, mana! Mu fa Allah Ya gaya mana a cikin qur’aninmu cewa:
﴿ وَأَعِدُّوا لـَهُم مَّاسْتَطَعْتُم مِّن قُوَّةٍ وَ مِن رِبَاطِ الـْخَيْلِ تُرْهِبُونَ بِهِ عَدُوَّ اللهِ وَعَدُوَّكُمْ
Ma’ana: Ku yi musu tattali na qarfi (makaman harbi) da turkakun dawakai don razanar da maqiyan Allah kuma maqiyanku

Amma abin mamaki gaba xaya musulman Najeriya mun yi shakulatin vangaro da wannan umurnin na Allah.
Su kuwa da Bible ya ce musu a cikin Luke 22: 36 “ …And he who has no sword, let him sell his garment and buy one.” Ma’ana: “…. Duk wanda ba shi da makami to, ya sayar da suturarsa ya sayi (makami).”  Sai ga shi har odar jirgin makamai su ke yi.  Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un

b) Zamantakewa da rayuwa
A sanadiyar rashin gwamnatin musulunci mai adalci, a yau mutanen Najeriya na rayuwa ne yadda suka ga dama. Har ta kai ga cewa idan mutumin kirki ya aikata wani aikin da addinin musulunci ya yi umurni da  shi, sai ka ji ana cewa ai su malam wane akwai takura ma kai. Dubi yadda zina, shan giya, luwaxi, maxigo su ka bayyana a qasar nan. Cin haramun da riba kuwa waxannan ‘yan gida ne. Abin takaici shine yadda matan aure suka nutsa cikin harkar zina. Aiki ba da ilimi ba kuwa ya zama ado a gunmu. Zumunta sai wane da wane. Son juna kuwa a baki ne kawai. ‘Yan uwantakar musulunci sai kaxan. Kar ma mutum ya yi maganar haxin kai don babu. Taimakon addini a wajenmu shine kawai mu gina masallatai, Don haka a yau muka cika anguwanninmu da garuruwanmu da masallatai waxanda kawai muke cika su jikinmu. Kamar  dai yadda Annabi (saw) ya ce: “……sun cika masallatansu da jikinsu amma zuciyarsu ta rushe daga shiriya.”  Dukkan waxannan halayen, rashin tsayayyar gwamnatin musulunci ya sa suka zama ruwan dare a qasarmu. Mafi munin al’amarin shine ba mu da wani jagora ma takamaimai mai faxa aji.
Ya ku musulman Najeriya babu shakka an fa ci mu da yaqi, duk wani abu da za’a yi mana a yau mai-mai ne. Jama’a an fa tsere mana, duk  wani sauri ko gudu da za mu yi don mu cimma waxancan, tafiyar guragu ce kawai.[3]   
TO YANZU INA MAFITA?
Mafitar ita ce
1) Fadin Allah Maxaukaki da yake cewa
﴿وَعَدَ اللهُ الَّذِينَ ءَامَنُوا مِنْكُم وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَيَسْتَخْلِفَنَّهُمْ فِى الْأَرْضِ كَمَا اسْتَخْلَفَ الَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُم دِينَهُمُ الَّذِى ارْتَضَى لَهُمْ وَلَيُبَدِّلَنَّهُمْ مِنْ بَعْدِ خَوْفِهِمْ أَمْنًا يَعْبُدُونَنِى وَلَا يُشْرِكُونَ بِى شَيْئًا وَمَنْ كَفَرَ بَعْدَ ذَالِكَ فَأُولَـــئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ۝ ﴾ سورة النور : ٥٥                                               
Ma’ana:                      
Allah Ya yi alqawari ga waxanda suka yi imani suka aikata aiki na qwarai cewa Zai sanya su, su zama mamaya a cikin qasa, kamar yadda Ya sanya waxanda suka zo kafin ku; kuma (Allah) Zai tabbatar musu da addinsu wanda Ya yardar musu a gare su; kuma Allah Zai canza musu bayan tsoron da suke ciki zuwa zaman lafiya, su bauta mini batare da suna haxa ni da kowa ba. Duk waxanda suka kafirce bayan wannan to, waxannan sune fasiqai.
    
Bari mu dubi  ayar nan da kyau
i.) Allah Ya yi alqawari ga waxanda suka yi imani suka aikata aiki na qwarai …..
babu shakka imani na gaskiya shine matakin farko na cin nasarar duniya da lahira. Aiki na kwarai kuwa Annabi (saw) ya yi bayaninsa a lokacin da aka tambaye shi wane aikin alheri ne ya fi kowanne? Sai ya ce: JIHADI DON XAUKAKA KALMAR ALLAH. (Muslim)
ii.) (Allah) Zai tabbatar mana da addinmu wanda Ya yardar mana a gare mu; kuma Zai canza mana tsoron da muke ciki zuwa zaman lafiya.
Alqawarin Allah da Ya yi mana a wannan ayar Ya yi ne bisa sharaxin in mun yi imani kuma mun yi aiki na qwarai.
Ashe ke nan matakin farko shine mu kyautata imaninmu, mu so juna so na haqiqa  wanda babu khiyana a ciki. Daga nan sai mu roqi Allah Ya ba mu jagora tsayayye wanda duk wani musulmi zai yi masa mubaya’a. wannnan shine ginshiqin da muka rasa don haka muka kasance cikin ruxu da hayaniya, kowa na abinda ya ke so.

2) Faxin Annabi (saw) da ya ce:
“Idan dai ku ka koma (ba abinda ku ka sani kuma ba abinda ku ke yi) sai noma da kiwo, ku ka bar jihadi; Allah Zai xora muku wani irin walaqancin da ba Zai cire muku shi ba har sai kun koma  zuwa ga  addininku (da gaske kamar yadda ya ke.)” Wannnan kuwa ba mai musun cewa haka muka koma a yau. Maza da mata yaro da babba ba abinda muka tasa a gaba sai neman duniya. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’una! A yau akwai matayen da ke kashe auren su don su koma makaranta, wai in sun gama su samu aiki a dama da su.

Allah Ka ba mu zaman lafiya mai xorewa. Ka qare mu da lafiyar da za ta zamo mana qarfi wajen rusa kafirci da zalunci a wannan qasar tamu mai albarka.


[1] Ban son in bayyana shawarar a nan soboda magabta
[2] Akan wannan maganar ne mu ka fitar da maqala mai suna jihadi na nan har tashin qiyama
[3] A wannan maganar na yi dungu a cikinta don bayyanata a zahiri zai sa magabta su ……………………………………

No comments:

Post a Comment